A shirye muke don zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasa - Shugaban INEC
Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman ƙanta a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumarsa a shirye take game da zuwa zaɓen zagaye na biyu na shugaban ƙasar idan har ba a samu wanda ya yi nasara a zagayen farko ba. Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kan shirye-shiryen hukumar na tunkarar babban zaɓen ƙasar da ke tafe a Chatham House da ke birnin Landan a Birtaniya. Ya ƙara da cewa a INEC ta yi shirin yiyuwar zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar, kamar yadda take yi a zaɓuka uku da suka gabata. Shugaban hukumar zaɓe ya kuma ce zaɓen ƙasar da za gudanar cikin wannan shekara zaɓe ne na matasan ƙasar. Farfesa Yakubu ya kuma ce rajistar masu kaɗa ƙuri'a ta nuna cewa matasa ne suka mamaye adadi mafi yawa na masu rajistar zaɓen. Shugaban Hukumar ya ce ya ji daɗin yadda mutane suka fito domin karɓar katinan zaɓensu, yana mai cewa fiye da mutum 600,000 sun karɓi katinansu a jihar Legas kaɗai cikin watan da ya gabata. Ya ƙara da cewa a yanzu adadin mas...