Posts

Showing posts with the label Jahar Ribas

Wike Ya Bawa Ma'aikata Hutu Domin Tarbar Tinibu A Ribas

Image
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ayyana Larabar nan a matsayin ranar hutu domin tarbar zaben shugaban kasa, Bola Tinudu a ziyarar da zai kai jihar. Wike, wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne da ke takun saka da dan takarar shguaban kasa na jam’iyyarsa, Atiku Abubakar, ya ce yayin ziyarar aikin ta kwana biyu, Tinubu zai kaddamar da gadar sama da ginin zamani da ya gina wa kottun Majistare a birnin Fatakwal, hedikwatar jihar. DAGA LARABA: Yadda Iyaye Ke Kashewa ’Ya’yansu Aure A Arewa La Liga: Barcelona ta yi wa Osasuna gida da waje a bana Wike wanda ya juya wa Atiku baya a zaben da Tinubu ya lashe, ya ce, “Ina kira ga daukacin al’ummar jihar su fito kwansu da kwarkwato su yi wa zabebban shugaban kasarmu kuma abin alfaharimu, Mai Girma Sanata Bola Ahmed Tinubu gagarumar tarba, tare da bayyana abin da aka san su da shi na karamci yayin a ziyarar da zai kaddamar da muhimman ayyukan ci gaba da za su zama tarihi. “Saboda haka na ayyana ranar Laraba, 3 ga Mayu 2023, a matsayin r