Na shiga matsananciyar damuwa da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan - Gwamnan Zamfara
Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook Inda yace "A madadin gwamnatin Jihar Zamfara, ina miÆ™a saÆ™on ta'aziyya da jaje ga al'ummar Æ™aramar hukumar Zurmi, musamman iyalai da ‘yan uwan waÉ—anda suka rasa rayukansu a harin ta'addanci da 'yan bindiga suka kai garin" Ina son tabbatarwa da al'umma cewa gwamnatina za ta bayar da tallafi da agajin gaggawa ga mutanen da abin ya shafa. Sannan ina mai tabbatar da cewa muna nan jajirce akan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar Zamfara baki É—aya. Ina sane da sadaukarwar da jami’an tsaro suke yi a Æ™oÆ™arin da suke na kare rayukan al’umma, gwamnatina za ta ba su duk wasu kayan aiki da kuma tallafin da suka dace domin yaÆ™ar ‘yan bindiga, ba za mu huta ba har sai Zamfara ta samu cikakken tsaro insha Allahu. WaÉ—annan sabbin hare hare sun biyo bayan nasarar da jami'an tsaro suka samu ne, na kashe shugabannin 'yan ta'addan. Ciki har da nasarar ...