An kori Farfesa daga aiki saboda nuna zanen hoton Annabi lokacin koyarwa
Jami’ar Hamline da ke birnin Minnesota na Amurka, ta kori wata Farfesa, Erika López-Prater, saboda nuna zanen Annabi Muhammad (S.A.W) yayin da take koyarwa.
A cewar rahotanni, wata daliba ce a ajin da take koyarwar ta yi korafi ga hukumar jami’ar.
An yi garkuwa da tsohon dan Majalisa a Edo
Isra’ila ta ba da umarnin cire tutocin Falasdinu daga gine-ginen gwamnati
Dalibar, mai suna Aram Wedatalla, ta shaida wa jaridar makarantar cewa ranta ya yi matukar baci da abin da malamar ta yi.
Aram dai wacce ’yar asalin kasar Sudan ce ta kuma ce ba za ta taba yarda ta zauna a cikin duk al’ummar da ba za ta mutunta abubuwan da ta yi amanna da su ba.
“A matsayina na Musulma kuma bakar fata, bana tunanin zan taba sakin jiki da kowacce irin al’ummar da ba ta mutunta ni kamar yadda nake mutunta ta,” inji ta.
Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito cewa Farfesar mai shekara 42, ta yi katobarar ce yayin wani ajin da take koyar da Tarihi, kodayake ta ce ta yi matukar taka-tsatsan kafin nuna zanen ga daliban.
Sai dai ta ce tun gabanin fara koyar da darasin, ta sanar da cewa za ta nuna hotunan Annabawa da sauran abubuwa masu tsarki, ciki har da na Musulmai da na addinin Buddha, kuma ta tambayi duk mai korafi a kai ya sanar da ita, amma babu dalibin da ya yi hakan.
Farfesar ta kuma ce ko a ajin ma, sai da ta sanar cewa za ta nuna hotunan na wasu ’yan mintuna, ko da wani daga cikin daliban na son ficewa saboda kada ya gani.
Sai dai malamar ta yi ikirarin cewa ba ta nuna hotunan domin cin zarafin Musulunci ba, inda ta ce hatta hotonta sai da ta nuna a lokacin da take dalibar jami’a a cikin ajin.