Posts

Showing posts with the label Dalar Amurka

Zamu Iya Mayarwa Da Maniyyata RararKudi Saboda Karyewar Dala- NAHCON

Image
Shugaban hukumar Alhazan Najeriya, Alhaji Jalal Ahmad Arabi ya ce akwai yiwuwar hukumar ka iya mayar wa maniyyata rarar kuÉ—in da suka biya sakamakon karyewar farashin dalar Amurka. Alhaji Jalal Arabi ya shaida hakan ne a wata hira da kafar sadarwa ta DCL da ke intanet wadda kuma hukumar alhazan Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ranar Alhamis. "Idan misali ranar da muka yi shela dala tana naira 1000, sai ya zamana kai ranar da ka saka kuinka ka saka ne ranar da take naira 900, to ai ka ga akwai ranar naira 100. Wannan naira 100 ya kamata ma mu maida maka. Ba mu jira tana ta yin asa ba. To idan kuma ta ara yin sama fa?" In ji Jalal Arabi. Ya ara da cewa "indai da rai da lafiya kuma idan dai mu ne a kan kujerar to ba za mu zauna a kan hakkin kowa ba da iznin Allah. Za mu tabbatar mun biya wannan rarar." To sai dai shugaban hukumar ta Alhazan na Najeriya ba faÉ—i lokacin da za a mayar wa da maniyyatan rarar kuÉ—aÉ—en nasu ba. A mafi yawancin lokuta dai hukum

Yadda Dalar Amurka Ke Jefa ’Yan Nijeriya Cikin Kunci

Image
Hauhawar farashin Dalar Amurka ya biyo bayan dokar da Shugaba Tinubu na barin Naira ta kwaci kanta a kasuwa. A ranar Litinin ta makon jiya ce Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Remi Tinubu ta kai ziyara Jihar Kano domin kaddamar tsangayar karatun lauyanci na Jami’ar Maryam Abacha, wato MAUN. A lokacin ziyayar ce Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ba wa Remi Tinubu sako ta sanar da mijinta cewa, al’ummar Nijeriyar na cikin halin kaka-nika-yi, saboda haka ya yi abin da ya dace. Sai dai tun a farko, Uwagidan Shugaban Kasar ta yi kira ga mutanen Nijeriya da su kwantar da hankalinsu, inda ta tabbatar da cewa lallai akwai haske da nasara a gaba. Idan ba a manta ba, tun a jawabin da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi lokacin rantsuwar karbar mulki, a ranar 29 ga watan Mayu ya bayyana cire tallafin man fetur, abin da ya haifar da karin kudin man nan take daga Naira 195 zuwa 540 a kan kowace lita daya. Sannan hauhawar farashin Dalar Amurka ya biyo bayan dokar da Shugaba Tinubu na barin Nai