Posts

Showing posts with the label Daliban BUK

Sanatan Kano Ya Ba Dalibai 620 Tallafin Karatu A BUK

Image
  Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kuma Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin ya ba wa daliban mazabarsa 628 tallafin karatu a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Aminiya ta gano cewa duk dalibin mazabar da ya rabauta ya samu tallafin N50,000 daga dan majalisar. Da yake bude rabon tallafin, shugaban ma’aikatan Sanata Barau, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi, ya ce dan majalisar ya yi haka ne domin ba wa daliban mazabarsa damar neman ilimi a manyan makarantu. Kakakin Mataimakin Shugaban Majalisar, Ismail Mudashir, ya ce daliban mazabar Kano ta Arewa da ke sauran manyan makarantu a fadin Najeriya ma za su amfana da tallafin. Don haka ya bukaci daliban da suka amfana da su yi amfani da abin da aka ba su ta hanyar da ta dace sanna su kara jajircewa wajen neman ilimi. Wani dalibin aji hudu a jami’a da ya samu tallafin , Adama Iliyasu Rabiu, ya yaba wa dan dan majalisar tare da rokon Allah Ya saka masa. (AMINIYA)

Gwamnan Kano Zai Biya Wa Daliban BUK 7,000 Kudin Makaranta

Image
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin biya wa daliban da ke karatu a Jami’ar Bayero (BUK) kimanin su 7,000 ’yan asalin Jihar kudin makaranta. Babban mai taimaka wa Gwamnan a kan harkokin kafafen sadarwa na zamani, Salisu Yahaya Hotoro, ne ya tabbatar da haka a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da maraicen Laraba. “Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin biya wa É—aliban jihar Kano da ke karatu a BUK su kimanin dubu bakwai kuÉ—in makaranta,” kamar yadda ya wallafa. Hakan na zuwa ne dai a daidai lokacin da daliban jami’ar ke ci gaba da kokawa da karin kudin da jami’ar ta yi. A sakamakon karin, dalibai da dama sun rika neman gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa musu. Hatta jami’ar ta Bayero sai da ta tsawaita wa’adin lokacin yin rajistar dalibai, kasancewar da dama daga cikinsu ba su iya kammalawa ba, saboda tsadar. (AMINIYA)