Posts

Showing posts with the label Mika mulki

Ba Ma Yi Wa Shirin Mika Mulki Zagon Kasa - Ganduje

Image
Gwamnatin jihar Kano  ta ce a shirye take domin miƙa mulki ga sabuwar gwamnati cikin ruwan sanyi ba tare da tayar da ƙura ba. Cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai Muhammad Garba, gwamnatin ta ce tuni aka samar da babban kwamiti da kuma ƙanana da za su taimaka domin ganin an miƙa mulkin salin alin. Ya musanta iƙirarin jam’iyyar NNPP da ta ke jiran karɓar mulki na cewa gwamnatin Ganduje na yi wa shirin miƙa mulki zagon ƙasa. Kwamishinan ya ƙara da cewa kwamitin miƙa mulki na ɓangaren gwamnatin Ganduje na rubuta rahoton ƙarshe kafin miƙa mulki. Ya bayyana cewa kamata ya yi kwamitin karɓa na gwamnati mai jiran gado shi ma ya shirya domin karɓar rahoton, wanda ya yi alƙawarin miƙawa a kan lokaci. Muhammad Garba ya ƙara da cewa manufar miƙa mulki shi ne gwamnati mai sauka ta miƙa duk wasu abubuwa na tafiyar da shugabanci cikin ruwan sanyi. Ba yunkurin yaɗa wani tunani ko wata aƙida ba. Ya kuma ce kamata ya yi gwamnati mai jiran gado t...