Gwamnan Kano Ya Soke Siyar da Asibitin Yara na Hasiya Bayero da Masaukin Gwamna Dake Birnin Kwankwasiyya
A ci gaba da kwato kadarorin al'umma da gwamnatin da ta shude a jihar ta siyar ba bisa ka'ida ba, Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya soke sayar da asibitin kananan yara na Hasiya Bayero da masaukin gwamna da ke birnin Kwankwasiyya. A cikin sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwaman, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, Gwamnan ya bayar da umarnin a gyara cibiyar lafiya cikin gaggawa tare da komawa aikinta a matsayin asibitin kwararru da ke kula da lafiyar dubban daruruwan yara daga jihar da ma sauran su. Gwamnan wanda ya jagoranci tawagar manyan jami’an gwamnati da suka kai ziyarar gani da ido a wuraren biyu da aka soke, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda gwamnatin da ta shude ta sayar da wuraren ga ‘yan gidan nasu saboda son kai. “Kamar yadda muka yi alkawari a lokacin gudanar da zaben, ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kwato kadarorin jama’a ko dai an karkatar da su ko kuma an sayar da su ta hanyar bogi, kuma abin da aka kwato za a yi