Posts

Showing posts with the label Kananan Hukumomi

Labari Da Dumiduminsa: Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kano Ta Sanar Da Ranar Zaben Kananan Hukumomi

Image
Shugaban Hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, shi ne ya sanar da hakan a safiyar ranar Laraba, yayin da yake yi wa manema labarai bayani  Malumfashi ya kara da cewa Hukumar za ta gudanar da zaben ne a ranar 30 ga Watan Nuwanba na 2024 Yayi amfani da taron wajen yin Kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki, su tallafawa Hukumar don gudanar da sahihin zabe Cikakken Labarin zai zo muku nan gaba 

Kwamitin Abba Gida-Gida Ya Gargadi Kananan Hukumomi Kan Almubazzaranci

Image
  Kwamitin KarÉ“ar Mulki na Gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi shugabannin kananan hukumomi 44 da ke jihar da manyan ma’aikatansu da su guji bari ana amfani da kudaden kananan hukumominsu ta hanyar da ta sabawa doka. Shugaban Kwamitin, Abdullahi Baffa Bichi ya ce gargadin ya zama dole domin kuwa sabuwar gwamnatin ba za ta lamunci yin almubazzaranci da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano ba. A cikin wata takarda da Babban Sakataren Watsa labarai na zababben gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, Baffa Bichi ya ce, “Mun sami labari cewa ana shirin amfani da kudaden kananan hukumomi wajen kammala zabuka a inda ba su kammala ba, a wasu kananan hukumomin Jihar Kano, wanda yin hakan ba dai-dai ba ne kuma ya saba wa doka.” Abdullahi Bafa Bichi ya ce gwamnati mai jiran gado a jihar ba za ta bari a É—auki kudaden al’umma a yi wa wata jam’iyyar siyasa aiki ba . AMINIYA

2023: Idan Na Zama Gwamna Zan Bawa Kananan Hukumomin 'Yancinsu - Gawuna

Image
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar  APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yi alkawarin baiwa kananan hukumomin jihar ‘yancin cin gashin kansu idan aka zabe shi a matsayin gwamna. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da shirin gidan talabijin na NTA cikin shirin "The Balot". "Ƙananan Hukumomin wani bangare ne na gwamnati kuma su ne matakin kusa da jama'a wanda ke taimakawa hatta ci gaba da rarraba albarkatu da ayyuka". "A matsayina na tsohon shugaban karamar hukumar na san abin da ya shafi gudanar da mulkinta". Lokacin da nake shugaban karamar hukuma, an ba ni cikakkiyar dama nayi  aiki. Hakan ya sa muka samu nasarori da dama don haka idan aka zabe mu a matsayin Gwamna zan mayar da martani kamar yadda Gawuna ya bayyana”. A sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Hassan Musa Fagge ya fitar, Gawuna Ya kara da cewa shi ne wanda ya fi cancanta kuma a shirye ya ke ya zama Gwamnan Jihar Kano bayan ya yi aiki