Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Jaddada Aniyarta Na Hada Gwiwa Da Majalisar Dokoki Ta Kano
Laminu Rabi’u Danbappa, ya bayyana hakan ne yau a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin majalisar kan harkokin aikin hajji a ofishinsa wanda ya kai ziyarar ban girma ga hukumar. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu,Laminu ya kara da cewa Hukumar Jin Dadin Alhazai, tana iya yiwuwa ne kawai idan aka hada hannu da juna domin kare abin da aka damka wa alhazai. A nasa bangaren, shugaban kwamitin alhazai na majalisar, kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar, Honarabul Sarki Aliyu Daneji, ya ce sun kasance a hukumar alhazai domin nuna fuskokinsu a matsayinsu na mambobin kwamitin daga majalisar dokokin jiha. Sarki Aliyu Daneji, yayi kira ga ma’aikatan gudanarwa da su bada hadin kai domin cimma burin da aka sanya a gaba. A nasa jawabin dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Dala a majalisar dokokin jiha Hon Lawan Hussaini Cediyar yan’gurasa ya shawarci hukumar alhaza...