Posts

Showing posts with the label TATTALIN ARZIKI

Fiye da mutane 85 sun mutu a turmutsitsin rabon kudi a Yemen

Image
  Akalla mutane 85 suka mutu, wasu daruruwa kuma suka jikkata, sakamakon tirmtsitsi da aka yi yayin wani taron raba kudade da aka yi a Sanaa, babban birnin kasar kasar Yemen da ke karkashin ikon ‘yan tawayen Houthi. Ya zuwa yanzu mutane 3 aka tsare bisa zarginsu da hannu wajen haddasa tirmitsitsin da sanyin safiyar ranar Alhamis, bayan da daruruwan mutane suka taru a wata makaranta domin karbar kyautar kudin Riyal din kasar ta Yemen 5,000, kwatankwacin dalar Amurka 8 da ake bai wa mutum guda guda, a daidai lokacin da watan Ramadan mai alfarma ya zo karshe. Hotunan bidiyo sun nuna yadda mutanen da mummunan cinkoson ya rutsa da su, suka rika tsala ihu da neman ceto sakamakon kasa motsawar da suka yi, yayin da wasu tsiraru suka rika yunkurin fitar da mutanen da suka ji rauni. Wasu hotunan bidiyon kuwa, sun nuna gawarwakin wasu daga cikin wadanda tirmitsitsin ya rutsa da su ne yashe a kasa, sai kuma tarin takalma da sauran nau’ikan tufafin da aka yi watsi da su, yayin da kuma wani mai ...

An sace gangan man fetur miliyan 17 a Najeriya

Image
  Wani sabon bincike da aka gudanar kan lamurran da ke wakana a fannin arzikin man Najeriya ya nuna cewar, an fitar da ganga sama da miliyan 17 na danyen mai daga kasar zuwa kasashen ketare ta barauniyar hanya, a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020. Rahoton da Andrew Ogochukwu Onwudili, babban jami’i mai binciken kudi na Najeriya ya fitar, wanda kuma jaridar   The Nation  da ke kasar ta ruwaito, ya kiyasta cewarkwatankwacin kudin danyan man fetur din da a iya cewa an sace daga kasar ya kai Dala Tiriliyan 1 da biliyan 20, da miliyan 969 da dubu 281. A cikin rahoton, an tuhumi  Ofishin Akanta-Janar na gwamnatin Najeriya da laifin biyan sama da Naira biliyan 73 ga jami’an da suke tantance inganci da adadin albarkatun mai da isakar gas din da ake shirin fitar da su daga kasar. Mai binciken yadda ake kashe kudaden Najeriyar ya bayyana cewar, kudaden da aka biya ba tare da an yi  kasafinsu ba, ya saba wa tanadin doka a sashi na 80(4) na kundin tsarin mulkin kasar na shek...