Posts

Showing posts with the label Kwankwaso

Kofa ya shirya taron addu'a na musammam ga Tinubu, Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf

Image
...Ya ce har yanzu ƙofar NNPP a buɗe take don yin ƙawance da APC da sauran jam’iyyu Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru da Bebeji, Kano, a yau ya tara malamai 1,000 a garinsa na Kofa a Bebeji, Kano, domin addu’a ta musamman ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kasar baki daya, Jagoran jam’iyyar NNPP da Ɗarikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE da kuma neman nasara ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a Kotun Ƙoli, da kuma addu’ar neman taimakon Allah ga ɗan majalisar.  A sanarwar da hadimin dan majalisar kan harkokin yada yada labarai, Sani Ibrahim Paki ya sanyawa hannu, yace yayin taron, malaman sun sauke Alƙur’ani sau 1,101, sannan suka yi addu’o’i na musamman. A taƙaitaccen jawabin da ya gabatar a wajen taron, Hon. Jibrin ya ce alaƙarsa da Shugaba Tinubu ba ɓoyayya ba ce. Ya kuma ce Kwankwaso ne maigidanshi, sannan zai ci gaba da iya ƙoƙarinsa wajen ganin an samu kyakkyawar alaƙa a tsakanin Tinubun da Kwankwaso.

Tinubu Ya Gana Da Ganduje A Abuja

Image
  Shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, ya gana da Gwamnan Jihar Kano mai barin gado, Abdullahi Umar Ganduje a gidansa na Defense House da ke Abuja. Da yammacin Asabar ɗin nan dai Ganduje ya shiga sahun waɗanda suka taro Asiwaju Tinubu lokacin da ya sauka Abuja daga ƙasar Faransa. Bayan an isa gida kuma sun yi ganawar sirri tsakaninsu. Ganawar dai ba ta rasa nasaba da ƙorafin da Ganduje yake da shi game da ganawar Asiwaju Tinubu da tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso a birnin Paris. A baya-bayan nan dai aka ji wani sautin hirar wayar tarho na yawo inda Ganduje ke kukan zaɓaɓɓen shugaban ƙasar bai kyauta masa ba da ya yi wannan tattaunawar. Kawo yanzu dai Ganduje bai bayyana wa manema labarai matsayar da suka cimma da Asiwaju Tinubu ba . AMINIYA

Da Sanin Ganduje Tinubu Ya Gana Da Kwankwaso —Kofa

Image
  Zababben dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce Gwamna Abdullahi Ganduje yana da masaniya game da ganawar da shugaban kasa mai jiran gado Bola Tinubu ya yi da Sanata Rabiu Kwankwaso a kasar Faransa. Aminiya  ta ruwaito yadda Tinubu da Kwankwaso suka yi ganawar sama da sa’o’i hudu a ranar Litinin. A wani sautin waya da aka nada, an ji Ganduje yana bayyana rashin jin dadinsa kan ganawar Tinubu da Kwankwaso, inda ya ce ya yi hakan ne a kashin kansa. An jiyo shi yana cewa ya kamata Tinubu ya tuntube shi ko kuma ya gayyace shi taron da ya yi da Kwankwaso. Sai dai a zantawarsa da Aminiya, Kofa, wanda ya halarci ganawar da shugabannin biyu suka yi a Faransa, ya ce Ganduje ya tabbatar masa da cewa Tinubu ya tuntube shi kafin a yi taron. “Na yi matukar kaduwa da na saurari sautin, amma ina ganin abu mafi muhimmanci shi ne ina son tabbatar muku cewa an tuntubi Gwamna Ganduje. “Kuma shi da kansa ya tabbatar min cewa zababben shugaban kasar ya gayyace shi, ya kuma shaida masa cewa

Abun Da Tinibu Da Kwankwaso Suka Tattauna A Kasar Waje

Image
Shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso a kasar Faransa. Wata majiya mai tushe ta ce Tinubu ya yi wa Kwankwaso tayin tafiya tare da shi a sabuwar gwamnati da kuma duba yiwuwar sulhu tsakaninsa da Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje. A ranar Litinin, mako biyu kafin Tinubu ya karbi rantsuwar fara aiki, suka shafe sama da awa hudu suna ganawar sirrin da Kwankwaso a birnin Paris na kasar Faransa. Majiyarmu ta ce a yayin ganawar, Tinubu ya bukaci hadin kai domin aiki tare da Sanata Kwankwaso — wanda ya lashe kuri’un Jihar Kano a zaben 2023. Kwankwaso da shugaban kasar da ke jiran rantsarwa nan da mako biyu masu zuwa sun kuma amince za su ci gaba da tattaunawa kan wannan batu. Majiyar ta ce mai dakin Kwankwaso da zababben Sanata Abdulmumini na Jam’iyyar NNPP ne suka raka madugun Kwankwasiyya zuwa wurin ganawar. A bangaren Tinubu kuma, matarsa, Sanata Oluremi da Mataimakin

Da dumi-dumi: Kwankwaso yayi ganawar sa’o’i hudu da Tinubu a birnin Paris

Image
Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya yiwa jam’iyyar NNPP a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, sun yi ganawar akalla sa’o’i hudu a birnin Paris na kasar Faransa a ranar Litinin, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito. A tsakiyar tattaunawar, TheCable ta fahimci cewa, akwai yuwuwar shigar Kwankwaso cikin gwamnati mai zuwa yayin da Tinubu ke shirin kafa “gwamnatin hadin kan kasa” – wanda ke nufin bai wa jam’iyyun adawa wasu mukamai a cikin gwamnatin. Taron ya kuma tattauna batutuwan da suka shafi zaben shugabannin majalisar kasa, gabanin kaddamar da majalisar ta 10 a ranar 13 ga watan Yuni. Zaben gwamnan kano: Inda aka Kwana game da karar APC da NNPP a Kotu An fara taron Paris tsakanin Tinubu da Kwankwaso ne da karfe 12:30 na rana kuma aka kammala da karfe 4:45 na yamma, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa jaridar TheCable. Ko Kun zabi aiki ko ba ku zaba ba, mun yi titin Kurna babban layi ne saboda All

Muna Kan Tataunawa Da Kwankwaso Da Obi - Atiku

Image
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) Rabi’u Musa Kwankwaso domin samun goyon baya da hadin gwiwa. A wata hira da BBC Hausa, Atiku ya ce yana kuma tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Ya ce ‘yan biyun Obi da Kwankwaso ba su da wata barazana ga damarsa a zaben. “Ban ga wata barazana domin ba ma tare da su (Kwankwaso da Obi). Muna cikin tattaunawa da su, watakila daya daga cikinsu ya zo,” inji shi. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian People Party (NNPP) Rabi’u Musa Kwankwaso domin samun goyon baya da hadin gwiwa. A wata hira da BBC Hausa, Atiku ya ce yana kuma tattaunawa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi. Ya ce ‘yan biyun Obi da Kwankwaso ba su da wata ba

Karon Farko A 2023 Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Ya Bayyana Babu Jar Hula

Image
A karon farko tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar NNPP, Senata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana babu jar hula. Sanata Rabi’u Kwankwaso ya bayyana cikin shigar Yarabawa a gangamin yakin neman zaɓensa na shugaban kasa da sauran yan takarkari a shiyyar kudu masu yammacin Najeriya da ya gudana a birnin Oyo da ke jihar Ibadan. Dantakarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar NNPP, Senata Rabi’u Kwankwaso da sauran jiga- jigan jam’iyyar A lokacin gangamin yakin neman zaben Senata Kwankwaso ya bukaci al’ummar jihar Ibadan da su zabi jam’iyyar NNPP a matakin kasa da jiha. Sanya jar hular dai wata alamace ta mabiya tsagin Kwankwasiyya – da ke goyon bayan tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso. Turawa Abokai Labarai24

Kuskuren Shekara 24 Ne Ya Jefa Najeriya Halin Da Ta Ke Ciki — Kwankwaso

Image
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kuskuren da shugabannin baya suka yi a shekaru 24 da suka shude ne ya jefa Najeriya cikin tsaka mai wuyar da ta ke ciki a yanzu.  Tsohon Gwamnan na Jihar Kano, ya bayyana haka ne a Landan yayin da yake amsa tambayoyi a ‘Chatnam House’ game zaben Najeriya na 2023. ’Yan takarar Gwamnan Kano sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya Dattijuwar da ta fi kowa tsufa a duniya ta rasu tana da shekara 118 A cewarsa, “Za mu iya alakanta kowane irin abu da ake zargin su ne ke da alhakin halin da muke ciki, tun daga annobar Kwarona zuwa koma bayan tattalin arzikin duniya da sauransu. “Amma a ni a ganina, mun fada halin da muke ciki ne saboda kuskuren da mutanen da aka dora wa alhakin mulkin Najeriya suka tafka a cikin shekaru 24 da suka gabata.” Kwankwaso wanda kuma tsohon Ministan Tsaron Najeriya ne, ya lissafa manyan matsaloli da kasar nan ke ciki da suka hada da rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, h

Zan mayar da Wa'adin Sakamakon JAMB Shekara 4 - Sanata Kwankwaso

Image
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso yayi alkawarin tsawaita wa’adin sakamakon jarabawar shiga jami’a (JAMB) zuwa shekaru hudu idan ya ci zaben shugaban kasa. Majiyarmu ta rawaito cewa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a Bauchi, lokacin da yake mika tutoci ga ’yan takarar gwamna shida da na Majalisar Dattijai 18 na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ranar Alhamis. An yi garkuwa da DPO a Filato Yadda aka yi wa Sakkwatawa kisan gilla a Anambra Kwankwaso ya ce dalibai da dama na samun sakamako mai kyau a rubuta jarabawar karo na farko, amma da zarar sun rasa gurbi a jami’a sai sun sake sabon lale bayan ba laifinsu ba ne. “Babu gaira babu dalili an sanya daliban da iyayensu lalubo kudin zana jarrabawa na shekaru biyu koma fiye. Haka ne ya sanya muku ga dacewar sauya haka. “Haka kuma za mu kirkiri sabuwar dokar dakatar da jarabawar JAMB din na tsawon shekaru hudu, domin ’ya’yanmu su yi amfani da sakamakon wajen samun gurbin karatu a manyan makarantun a w

Duk wanda ya yake ni Sai ya gane kurensa - Kwankwaso

Image
Dan karar shugaban kasa na Jam’iar NNPP, Sana Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce duk wanda ya yake shi a Jihar Kano a zaben 2023, sai ya yaba wa aya zaki. Jaridar Aminiya ta rawaito cewa Kalaman tsohon gwamnan jihar na zuwa ne bayan gwamna mai ci kuma wanda ba sa ga maciji, Abdullahi Ganduje, ya ce wa magoya bayan Jam’iyyar APC, a 2023 Kano za ta maimaita abin da ta yi a zaben shugaban kasa na shekarar 1993. Ana ganin kalaman na Ganduje tamkar gugar zana ce cewa Kananawa ba za su zabi Kwankwaso ba a zaben da ke tafe a ranar 25 ga waan Fabrairu. Amma a martanin Kwankwaso, ya ce, “Ba na son kula wancan mutumin, ban san ko ya fada ko bai fada ba, amma duk wanda ya yaki NNPP ko Kwankwaso a 2023 sai ya i da-na-sani.” Ya ci gaba da cewa, “Duk wanda ya san ni, ya san abin da na yi a baya, ya san idan na ci zaben shugabna kasa, Kano za ta fi kowa amfana, Arewa za ta amfana, haka kuma kasa baki daya.” A cewarsa, “Kwanan nan yi gangamin yakin neman zabe wadanda ke cikin mafiya kayatarwa, b