Posts

Showing posts with the label Ranar malamai ta duniya

Ranar Malamai Ta Duniya 2023: Gwamna Abba Kabir Ya Jinjinawa Malaman Kano

Image
A yayin da al’ummar duniya ke bikin ranar malamai ta duniya 2023 a yau wadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin gudanar da bikin ranar 5 ga watan Oktoban kowace shekara, Gwamnan Jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf ya yi kira ga malaman jihar da su jajirce wajen ganin sun kammala aikinsu. A sanarwar da babban sakataren Yada labaran gwamnan, Sunusi Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, Gwamna Abba Kabir Yusuf a lokacin da yake tsokaci kan kokarin malamai na tunawa da ranar malamai ta duniya ta bana, Gwamnan ya bayyana su a matsayin masu gina kasa wanda dole ne kowace gwamnati mai kishin kasa ta ba su kulawa sosai. Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce ba za a iya karawa da irin gudunmawar da malamai suke bayarwa ba domin su ne mataki na ginshikin horar da ma’aikatan da suke daukaka a kowane fanni na ayyukan dan Adam. Alh Abba Kabir ya jaddada shirye-shiryen gwamnatin sa na inganta koyo da koyarwa ta hanyar gaggauta biyan albashi, karin girma, horaswa, sake horarwa da sa...