Birtaniya Ta Gurfanar Da Diezani A Gaban Kotu Kan Zargin Almundahana
Kasar Birtaniya ta gurfanar da tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke a gaban kotu kan zargin rashawa lokacin da take Minista. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ’yan sandar kasar sun ce sun maka ta a kotun ne saboda suna zargin ta karbi cin hanci a wasu kwangilolin man fetur da iskar gas. Diezani, mai shekara 63 a duniya, na daya daga cikin kusoshi a gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan. A zamanin mulkin tsohon Shugaban, Diezani ta rike mukamin Ministar Mai ta Najeriya daga 2010 zuwa 2015, sannan ta rike matsayin shugabar Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur ta Duniya (OPEC). A cewar Shugaban Hukumar Yaki da Laifuffuka ta Birtaniya (NCA), Andy Kelly, “gurfanarwar da aka yi wa Diezani wata somin-tabi ce na wani zuzzurfan bincike na kasa da kasa da aka dade ana yi.” Hukumar dai ta ce ana zargin Diezani da karbar akalla tsabar kudi har Fam din Ingila 100,000 da wasu motoci da hawa jirgin da ba na ’yan kasuwa ba, ...