Posts

Showing posts with the label Ahmed Mirwa Lawan

Lawan Majakura: Mai Sayar Da Kifi Da Ya Kada Shugaban Majalisar Yobe

Image
  A zaben Gwamna da na ’yan majalisar jiha da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga Maris ne Lawan Musa Majakura mai shekara 33, ya kayar da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Yobe, Alhaji Ahmed Mirwa Lawan da kuri’a 182 don wakiltar Mazabar Nguru II a Karamar Hukumar Nguru a Jihar Yobe. Majiyarmu  ta tattauna da zababben dan majalisar na Jam’iyyar PDP ta waya, inda ya yi bayani kan takaitaccen tarihi da harkokin siyasarsa da yadda ya samu nasarar da ta yi waje da Shugaban Majalisar: Mene ne takaitaccen tarihinka? An haife ni a garin Majakura da ke Karamar Hukumar Nguru a watan Janairun 1990. Na yi karatun firamare a Majakura. Daga nan na wuce Kwalejin Gwamnati da ke Nguru, inda na samu karamar Diploma a Nazarin Addinin Musulunci. Daga nan na tafi Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya da ke Damaturu, inda na kammala a shekarar 2009 tare da samun takardar Babbar Diploma (HND) a fannin kasuwanci da Gudanarwa a 2020. To amma ban samu damar yi wa kasa hidima ba (NYSC) saboda shekaruna su...