Posts

Showing posts with the label Mawaki

Hukumar Tace Finafinai Ta Rufe Sutudiyon Mawaki Ɗanzaki

Image
Hukumar Tace Finafinai da Dab’i ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa ita ce ta garƙame sutudiyon mawakin siyasar nan Idris Ɗanzaki tare da yin awon gaba da kayan aikinsa. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Abdullahi Lawan Sulaiman ya shaida wa ’yan jarida a Kano cewa hukumar ta ɗauki matakin ne bayan mawaƙin ya yi biris da gayyatar da ta yi mana na bayyana a ofisoshint Ya ce tun ranar Asabar Hukumar ta nemi mawakin ya bayyana a ofisoshinta, amma har zuwa lokacin da muke kawo muku wannan labari bai amsa gayyatar ba. “Kasancewar a yanzu zamani ya sawwake abubuwa mun yi amfani da waya inda muka kira wannan mawaki Idris Ɗanzaki inda kuma muka nemi ya zo wannan hukuma. “Bayan sun kira ni a waya sun ce suna gayyata ta, na tura lauyana hukumar don ya wakilce ni. “Amma me zai faru sai aka kira ni cewa wai hukumar ta rufe sutudiyona haka kuma ta kwashe wasu kayayyakin aikina.” Abdullahi Lawan ya kara da cewa hakan ya sa Hukumar ta sa aka kulle sutudiyon tare da kwashe kayayyakin aikin