Posts

Showing posts with the label Babban Bankin Najeriya

Hajj 2024: CBN Ya Janye Batun Biyan Kudin Guzurin Alhazai Ta Katin ATM

Image
Babban Bankin Najeriya ya dakatar da bayar da guzurin Alhazai na Hajji 2024 ta hanyar katin ATM Kwafin takardar da Bankin ya fitar wacce kuma  HAJJ REPORTERS ta gani mai kwanan wata 17 ga Mayu 2024 mai dauke da sa hannun daraktan riko na sashen ayyuka na kudi Solaja Muhammed J. Olawumi wanda aka aikewa bankunan kasuwanci ya ce “bayan gaggawar da aka samu tare da lura da karancin lokaci dangane da jigilar jirgin. Alhazan 2024, Shugabancin Bankin ya amince da biyan dukkanin tsabar kudi ga maniyyatan. “Ku lura cewa wannan sanarwar ta zarce tsarin da aka gabatar muku na farko na ayyukan Hajji na 2024. Nan ba da jimawa ba za a mika wata wasika a hukumance kan hakan.” Idan dai za a iya tunawa babban bankin ya sanar da hukumar alhazai ta kasa NAHCON da Jihohi da Rundunar Soji cewa za a biya kudin guzurin na Hajjin bana  wanda aka biya dala 500 ga kowane mahajjaci da kashi 60/40 cikin 100. tsabar kudi da kati Bankin ya ce dala 200 ne kawai za a ba da tsabar kudi yayin da z...

Hajj 2024: Kungiyar Fararen Hula Ta Yi Kira Ga Babban Bankin Najeriya Ya Sauya Tunani Kan Biyan Kudin Guzurin Alhazai

Image
An shawarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya yi watsi da ra’ayin bayar da kudin  (BTA) ta hanyar katin biyan kudi. Kungiyar fararen hula masu daukar rahotannin aikin Hajji  (IHR) ne suka bayar da wannan shawarar a wata sanarwa da babban jami'inta na kasa Ibrahim Mohammed ya fitar. Kungiyar ta ce kasa da sa’o’i 24 da fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki, babban Bankin ya umarci wasu bankunan kasuwanci da su biya maniyyatan dala 200 kacal daga cikin dala 500 da ake sa ran kowane mahajjaci zai samu yayin da sauran dala 300. za a bayar a kan katin cirar kudi  “Alhazai na bana sun riga sun shiga cikin rashin tabbas da yawa tun daga manufofin sayayya da suka haifar da hauhawar farashin Hajji zuwa raguwar kudin guzuri. Wannan shawarar da babban bankin ya yanke zai kara musu bala’i ne kawai”. “ Sanin kowa ne cewa mafi yawan alhazanmu sun fito ne daga karkara kuma ba su da masaniyar harkar hada-hadar kudi, yawancin ma ba su san yadda ake amfani da katin ATM...

CBN Ya Soke Lasisin ’Yan Canji 4,173 A FaÉ—in Nijeriya

Image
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin gudanar da ayyuka na wasu ’yan canji 4,173 a faÉ—in Æ™asar nan take. CBN ya ce daga cikin ’yan canjin da soke lasisin ya shafa akwai waÉ—anda suka gaza sabunta lasisinsu, da waÉ—anda suka gaza biyan wasu caje-caje kuÉ—in gudanarwa da Babban Bankin ya rataya a wuyansu. Haka kuma, daga cikin waÉ—anda abin ya shafa akwai masu bijire wa dokokin Babban Bankin kan tsare-tsarensa na yaÆ™i da safarar kuÉ—aÉ—en haram, dakile fitar da kuÉ—aÉ—en da ke É—aukar nauyin ayyukan ta’addanci, da kuma dakile ka’idojin samar da kuÉ—aÉ—e. Kazalika, CBN ya ce waÉ—anda aka soke wa lasisin akwai masu rashin mika wa CBN É—in bayanan yadda suke sayar da dalar duk mako. Wannan matakin wani É“angare ne na Æ™oÆ™arin da CBN da Gwamnatin Tarayya ke yi na maido da Æ™warin gwiwa a kasuwar canji da musayar kuÉ—aÉ—en waje da kuma farfaÉ—o da tattalin arzikin Æ™asar. CBN dai ya yi alÆ™awarin ci gaba da bayar da dala ga masu kamfanin canjin kuÉ—in a kowanne mako kamar yadda aka saba...

Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Image
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele. Wannan dai ya biyo bayan binciken ofishinsa ne da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar. Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya fitar, ta ce an umurci Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Mataimakin Gwamna (Directoral Directorate), wanda zai rike mukamin Gwamnan Babban Bankin. ana jiran kammala bincike da gyare-gyare. NTA 

Labari da dumiduminsa : Bankin CBN Ya Ce Za A Ci Gaba Da Amafani Da Tsofaffin Kudi Na Har Zuwa 31 Ga Disamba

Image
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce tsofaffin takardun kudi na N200, N500 da N1000 suna nan a kan doka har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023. Kakakin CBN, Isa Abdulmumin ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Litinin. “A bisa bin ka’idar da aka kafa ta bin umarnin kotu da kuma biyan ka’idar bin doka da oda da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi, da kuma karawa ayyukan Babban Bankin Najeriya (CBN), a matsayin mai kula da Deposit. An umurci bankunan kudi da ke aiki a Najeriya da su bi hukuncin da kotun koli ta yanke na ranar 3 ga Maris, 2023,” in ji sanarwar. “A bisa haka, CBN ya gana da kwamitin ma’aikatan banki inda ya ba da umarnin cewa tsofaffin takardun banki na N200, N500 da N1000 su ci gaba da zama a kan takardar kudi tare da sake fasalin kudin har zuwa ranar 31 ga Disamba, 2023.

Daga yanzu Bankuna Zasu Rinka Bayar da Sababbin Kudi A Kan Kanta

Image
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce daga yanzu Bankuna Zasu rinka bawa mutane kudi a kan Kanta, sabanin umarnin da ya bayar na baya kan cewa sai a Na'urar ATM kadai zasu sanya kudaden domin masu hulda dasu su cira. Hadimin Shugaban kan harkokin kafafen yada labarai na yanar Gizo, Bashir Ahmed ne ya wallafa wannan labari a shafinsa na Instagram  Za a iya tunawa cewa A ranar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ya gana da Shugaba Buhari ne ya fitar da sabuwar sanarwar da ta ce ko bayan Karewar Wa'adin kashe tsofaffin kudi, Bankuna Zasu ci gaba da karbarsu domin mikawa Babban Bankin 

Da dumi-dumi: CBN ta kara wa’adin karbar tsofaffin kuÉ—in

Image
  A karshe dai babban bankin Najeriya CBN ya kara wa’adin daina karÉ“ar tsofaffin kudi har zuwa nan da kwanaki 10.   Majiyarmu ta rawaito a wata sanarwa da gwamnan babban bankin na CBN, Godwin Emefiele ya fitar a ranar Lahadi, ya ce sabon wa’adin zai kare ne 10 ga watan Fabrairun 2023. Duk da haka, har yanzu ’yan Najeriya za su iya mika tsofaffin takardun Kudinsu kai tsaye zuwa bankin CBN har nan da ranar 17 ga Fabrairu, 2023.   Talla daukar nauyi Suraj Umar Wudil ‘Yan Najeriya dai sun yi ta kokawa kan rashin wadatattun sabbin kudin wanda da farko aka ce wa’adin zai kare a ranar 31 ga watan Janairu . A baya dai CBN ta ce ba za ta kara wa’adin ba.  

Babban Bankin Najeriya Ya Ce Ya Kashe Dalar Amurka Biliyan 11.42 Don Farfado Da Darajar Naira

Image
Rahoton da babban bankin Najeriya ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya ce bankin ya kashe dalar Amurka biliyan 11.42 a cikin watanni 7, daga watan Janairu zuwa watan Yuli na shekarar 2022 domin a farfado da darajar naira. Masana tattalin arziki da kwararru a fannin hada-hadar kudi na ganin wannan kokari da bankin CBN ya yi bai hana matsalar canji tsakanin dalar Amurka da naira ba, hasali ma har yanzu farashin kayan masarufi na karuwa a kasuwanni. Ya zuwa wannan lokacin, ana sayar da dalar Amurka daya a kan naira 750 a kasuwar bayan fage yayin da a banki kuma ake sayar da dalar kan naira 450, bambancin naira 300 kenan tsakanin banki da kasuwar bayan fage. A hirar shi da Muryar Amurka, Umar Garkuwa, daya daga cikin manyan ‘yan canjin kudi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya ce karyewar naira laifin babban bankin kasar ne ba laifin ‘yan canji ba. Garkuwa ya ce matsalolin harkar canji a Najeriya ba kamar a wasu kasashen duniya ba ne, domin lamarin ya zama wata harka da ...

Babu Gudu Ba Ja Da Baya Kan Wa’adin Tsofaffin Kudade – Emefiele

Image
Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ce babu gudu babu ja da baya kan wa’adin daina karbar tsofaffin takardun kudade a ranar 31 ga watan da muke ciki. Emefiele ya jaddada kudurin babban bankin na daina amfani da kudade a ranar Talata a Abuja. Mun lalata miyagun kwayoyi na N95bn a Kwatano – NAFDAC ‘An kashe ’yan sa-kai 1,773 a rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas’ Ya ce “Ba ni da wani sabon labari ga wadanda suke so a tsawaita kwanakin daina karbar tsofaffin takardun kudade. “Mutane sun tara kudade a gidajensu kuma suna sane da cewar ba su da lasisin yin hakan.” Ya ce CBN ya samu nasarar karbar sama da tiriliyan 1.5, kuma yana sa ran cimma tiriliyan 2 kafin wa’adin ya cika a karshen watan nan. Ya ce “Mun roki Hukumar Yaki Da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zangon Kasa (EFCC) da Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa (ICPC) da kada su musgunawa kowa kan mika tsofaffin kudaden bankuna, kuma saboda ni sun tabbatar da min ba za su yi komai ba,” in ji shi. Wannan d...