Kungiyar Kannywood Ta Bawa Kwamishinan Kudi Na NAHCON Lambar Yabo
Da yake jawabi, jagoran tawagar Alhaji Ahmed Kaka ya taya hukumar murnar kammala aikin Hajjin 2023 cikin nasara duk da kalubalen da ake fuskanta. A sanarwar da Shafi'i Sani Muhammad na sashen yada labarai da Dab'i na Hukumar NAHCON ya sanyawa hannu, Shugaban kungiyar ya yi kira da a hada kai a tsakanin bangarorin guda biyu musamman ta fannin wayar da kan alhazai da tsawaita amfani da kafafen sada zumunta na zamani. Kungiyar ta baiwa Alhaji Nura Hassan Yakasai, Kwamishinan kudi lambar yabo ta taimakon jin kai bisa gudunmawar da ya bayar wajen bayar da muhimmin taimako ga marasa galihu a cikin al’umma. Alhaji Yakasai wanda ya bayyana jin dadinsa ga dandalin ya tabbatar musu da shirye-shiryen Hukumar na yin bincike da hada kai da kungiyar nan gaba. Tunda farko da yake nasa jawabin, Shugaban Hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya yi kira ga ‘yan wasan kwaikwayon Najeriya da su ci gaba da amfani da kafar sadarwar su wajen wayar da kan ‘yan Nijeriya musamman Alh...