Sabon babban sakataren shari’a na jihar Kano, Alhaji Sanusi Abbas, wanda kuma dan gidan marigayin ne ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Justice Watch ta ruwaito.
A cewarsa, marigayi Hakimin Kauye kuma uba ne ga shugaban karamar hukumar Rimin Gado na yanzu, Barista Munir Dahiru Maigari.
“Marigayi Maigari ya rasu ne bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wa gidansa hari da sanyin safiyar Lahadi, inda suka yi masa raunuka daban-daban daga bisani suka harbe shi har lahira.” Yace.
Ya kuma kara da cewa za a yi jana’izar ne a yau a gidansa da misalin karfe 10 na safe a kauyen Maigari da ke karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano.
“Allah ya sa ransa ya huta a Aljannatur Firdous,” in ji Sakataren dindindin.