Posts

Showing posts with the label Majalisar Dokokin Kano

Majalisar Dokoki Ta Kano Ta Amince Da Mutum 20 Da Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Mika Mata Don Nadasu Masu Bashi Shawara Na Musamman

Image
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da nadin mukamai na musamman guda ashirin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi. Jaridar Daily News 24 ta ruwaito cewa ta Sahalewa Gwamnan ne a yayin wani zama da shugaban majalisar, Ismail Jibrin Falgore ya jagoranta bisa tsari na 196/2 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya. Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Majalisar, Uba Abdullahi ya fitar ta ce amincewar ta biyo bayan wasikar da Gwamnan ya aike wa majalisar na neman nadin wanda aka tattauna a gaban zauren majalisar tare da cimma matsaya. Majalisar ta dage zamanta zuwa ranar 19 ga watan Yuni, 2023 a wani kudiri da shugaban masu rinjaye Hon Lawan Husaini na mazabar Dala ya gabatar kuma shugaban marasa rinjaye, Labaran Abdul Madari na mazabar Warawa ya mara masa baya.

Labari da dumiduminsa : Jibrin Falgore ya zama kakakin majalisar dokokin Kano

Image
Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Rogo a majalisar dokokin jihar Kano, Jibril Samaila Falgore, ya zama shugaban majalisar dokokin jihar. Muhd Bello, mataimakin kakakin majalisar Prime Time News ta tattaro cewa an zabi Falgore a matsayin kakakin majalisar bayan wata tattaunawa da ‘yan majalisar suka yi. Lawal Hussaini,. shugaban masu rinjaye Taron wanda aka gudanar a ranar Litinin din da ta gabata don kammala tabbatar da sabbin shugabannin majalisar dokokin jihar ya samu halartar gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdusalam Gwarzo, shugaban jam'iyyar na kasa, Engr Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran su. Sabon shugaban majalisar ya fito ne daga mazabar Kano ta Kudu kuma shi ne dan takarar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga shiyyar. Muhd Bello, mataimakin kakakin majalisar, Muhammad Bello Butu Butu daga mazabar Rimin Gado ya zama mataimakin kakakin majalisar, yayin da mukamin shugaban masu rinjaye ya koma Lawan Husaini na m...