Sufeto Janar Ya Sake Turo Usaini Gumel A Matsayin Sabon Kwamishinan 'Yan Sanda Na Kano
Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali, ya sake soke turo kwamishinan ‘yan sandan Kano. A wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, Sufeto Janar din ya soke aika Feleye Olaleye a matsayin kwamishinan ‘yan sandan Kano tare da sanya CP Ahmed Kontagora a matsayin wanda zai maye gurbinsa. Sai dai a wata siginar da aka sake fitarwa a daren jiya, sufeto janar din ya nada CP Usaini Gumel a matsayin wanda zai jagoranci rundunar 'yan sanda ta Kano lokacin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a jihar. A ranar 8 ga Maris, bayan zanga-zangar da ‘yan adawa suka yi, IGP ya sauya matakin da aka tura CP Balarabe Sule, tsohon babban jami’in tsaro ga gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, a matsayin wanda zai maye gurbin CP Mohammed Yakubu A cikin sabuwar takardar da aka fitar mai dauke lamba TH.5361/FS/FHQ/AB3/SUB.6/146, Mista Alkali kuma ya sake yin wasu Æ™ananan canje-canje a cikin umarnin. IGP ya umurci DCP Auwal Musa da ya karbi DCP Nuhu Darma a matsayin mataimakan kwamishin...