Yau sabuwar majalisar Amurka za ta yi zamanta na farko

A yau Talata sabuwar majalisar dokokin Amurka za ta fara aiki inda dan Republican Kevin McCarthy zai nemi zama shugaban majalisar wakilai.

Bayan zaben rabin wa’adi da a aka yi a watan Nuwamba, ‘yan Republican sun karbe ragamar shugabancin majalisar wakilai amma da dan kankanin rinjaye.

Majalisar dokokin Amurkar a wannan ta rabu gida biyu, inda ‘yan Democrat suka ci gaba da rike shugabancin majalisar dattawa yayin da ‘yan Republican suke karbe majalisar wakilai.

Wani abu da zai fi jan hankali a yau shi ne yadda ‘yan Republican za su zabi shugaban majalisar ta wakilai.

McCarthy na fatan ganin ya gaji Nancy Pelosi ‘yar Democrat amma kuma yana fuskantar kalubalen rashin samun goyon baya - har daga abokansa.

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 100 da dan takarar neman shugabancin majalisar wakilai ya gaza samun goyon baya daga wasu ‘yan jam’iyyarsa.

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump na goyon bayan McCarthy.

Dan majalisar wakilai Andy Riggs na jihar Arizona da Steve Scalia mai wakiltar Louisiana na daga cikin ‘yan Republican din da suke adawa da McCarthy.

Bayanai sun yi nuni da cewa daukacin ‘yan Democrat ba za su goyi bayan McCarthy ba, abin da ke nufin dole sai dai ya mayar da hankalinsa kan kuri’un ‘yan Republican.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki