Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba — Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa
Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano mai Yaƙi da Shan Miyagun Kwayoyi da Safarar Su Ba Bisa Ka'ida ba, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan siyasa da su daina neman a saki 'yan daba ko waɗanda ake zargi da laifukan da suka shafi miyagun kwayoyi bayan an kama su. Da yake zantawa da manema labarai a Kano, Rimingado ya ce kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin adalci ba tare da nuna son kai ko tsoro ba, yana mai jaddada cewa ba zai bari wani tasirin siyasa ya kawo cikas ga yaƙin da ake yi da shan miyagun kwayoyi, safarar su da kuma ayyukan 'yan daba ba. Ya ce babu wani ɗan siyasa da ya kamata ya zo neman a saki duk wani wanda aka kama da laifuka. "Kada wani ɗan siyasa ya zo wurina yana neman na saki ɗan daba idan muka kama shi. Wannan Kano ce, kuma dukkanmu 'yan asalin jihar ne. Ba za mu bari wasu tsirarun mutane su lalata makomar jiharmu ba." Rimingado ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ...