Kamawa zasu maimaita abun da ya faru a zaben 1993 - Ganduje

Abdullahi Umar Ganduje, ya ce Kanawa za su sake maimaita abin da ya faru a zaben Shugaban Kasa na 1993, inda suka goyi bayan dan takarar da ya fito daga yankin Kudu – suka yi watsi da nasu na Arewa kuma dan asalin jihar.

Ganduje ya yi wannan furuci ne a yayin wani rangadin yakin neman zabe da ya fita tare da ’yan takarar jam’iyyar APC masu neman mukamai daban-daban a zabe mai zuwa.


Aminiya ta ruwaito cewa gwamnan ya yi furucin ne yayin da ya ziyarci Hakimin Kibiya, Sunusi Abubakar Ila, bayan gudanar da taron yakin neman zabe da tuntubar juna a kananan hukumomin Rano da Bunkure na jihar.

A zahiri dai Ganduje ya tabbatar da goyon bayansa ga dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, inda ya yi hannun riga da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ke takarar kujerar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP.

A jawabinsa yayin hikaito tarihi, Ganduje ya ce, “Mun zabi Cif MKO Abiola na jam’iyyar SDP kuma muka ki amincewa da Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC saboda dukkanmu mun yi imani da hadin kan kasa da la’akari da cancanta.

“Sanin mu ne cewa Tinubu ya kasance ginshiki wajen fitowar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar Action Congress (AC).

“Ya [Tinubu] kuma tsaya tsayin daka wajen ganin Nuhu Ribadu ya zama dan takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).

“Saboda haka, Asiwaju Tinubu ya yi aiki tukuru wajen ganin an samu daidaito, kuma a baya ya rika fadi–tashi wajen goyon bayan ’yan takarar Shugaban Kasa da suka fito daga a Arewa.

“Duba da wannan dalili, ya cancanci mu saka masa da irin alherin da ya yi. Kuma a yanzu ba mu da wani zabi da ya wuce mu goyi bayan takararsa.

“A halin yanzu Tinubu shi ne daya tilo wanda ya cancanta kuma ya fi cancantar takarar Shugaban Kasa a zabe mai zuwa.

“Ba zai gushe ba Arewa na goyon bayansa saboda akidarsa ta gina kasa, da sanin ya kamata, da tsayuwar daka ga ci gaban bil’adama da kasa, da dai sauran abubuwa,” in ji Ganduje.

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki