Hajin bana: Hukumar kula da jin dadin alhazai ta jahar Kano za ta fara gudanar da bita ga maniyyata aikin haji nan da mako biyu

 

 

Tun bayan da aka kammala aikin Hajin 2022, Hukumomin Hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) da sauran hukumomin jin dadin alhazai na Najeriya, suka fara tunkarar aikin hajin shekara ta 2023 domin gujewa sake afkuwar matsalolin da aka samu a aikin hajin da ya gabata 


Ana tsakiyar wadannann shirye-shirye ne katsam sai hukumar kula da aikin Haji da Umrah ta kasar Saudi Arabia ta bayyana sake dawowa da Najeriya yawan adadin kujeru dubu casa’in da biyar da (95,000) da ta saba bata tun kafin bullar cutar Covid-19 

Da yake yi wa manema labarai jawabi a ofihinsa, Sakataren zartawa na hukumar kula da jin dadin ta jahar Kano, Alhaji Muhammad Abba Dambatta, ya ce ya zuwa yanzu hukumar ta mayarwa da kaso fiye da casa’in da tara na maniyyatan da basu samu zuwa aikin hajin da ya gabata ba kudadensu 


Alhaji Muhammad Abba ya bayyanawa maneman labaran cewa tuni hukumar ta kammala dukkanin shiri domin fara gudanar da bitar alhazai a tsakiyar watan Janairun da ake cikin 

Dambatta yayi kira ga maniyyatan da suka bar kudadensu ga hukumar, dasu gaggauta zuwa domin sake sabunta ragistarsu ta koma ta wannan shekara da muke don gujewa samun matsala da ka iya faruwa 


Sakataren zartarwa ya kara da cewa a yanzu haka hukumar aikin Hajin Saudi Arabia ta gayyaci jami'an hukumar NAHCON da dukkanin shugabannin hukumomin alhazai na jahohi domin sake tattaunawa kan shirin aikin hajin bana 


Ya kuma bayyana cewa ana sa ran maniyyata aikin hajin bana na Najeriya zasu fara tashi zuwa kasa mai tsarki daga ranar 4 ga watan Mayu na wannan shekarar da muke ciki, inda ya sanar da cewa tuni kasar Saudia ta sake samar da karin filin saukar jirage sababbi guda biyu a birnin Madina 


Daga nan sai ya yi kira ga dukkanin masu son zuwa aikin hajin na bana dasu gaggauta biyan kudinsu tun kafin lokacin ya kure musu domin a cewarsa har yanzu hukumar na ci gaba da karbar kudin kujerar na aikin hajin bana 

Popular posts from this blog

Yanzu - Yanzu: Bankuna Zasu Karbi Tsofaffin Kudi Ko da Bayan Karewar Wa'adi - Emefiele

Zababben Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Karbar Mulki