Posts

Showing posts with the label Ruqayya Jibia

Ya Kamata A Yi Wa Ruqayya Aliyu Jibia Adalci - Nasir Salisu Zango

Image
Daga Nasir Salisu Zango  Ruqayya Aliyu Jibia’yar jarida ce dake wakiltar gidan talabijin na Tambarin Hausa a jihar Katsina,kuma a kwanakin nan ta samu sabani da ‘yansandan jihar Katsina bayan da ta wallafa bidiyo a shafin ta na TikTok wanda a ciki ta bayyana rashin da cewar abin da ‘yansanda keyi na sakin bidiyon wadanda ake zargi da laifi musamman yadda ake nuna fuskokin su. Amma abin takaici bayan sakin bidiyon sai Ruqayya tayi kukan cewar, ‘yansandan sun ci zarafin ta har ma an kama ta an fasa mata waya an kuma kai ta gaban sarkin Katsina wanda acan ma tace an yi tayi mata barazana. Kamar yadda ta bayyana. Na dai tuntubi mai magana da yawun rundunar‘yansandan jihar Karsina CSP Gambo Isa wanda yace min Abin da Ruqayya take musu akan aikin su bai dace ba. Babban abin takaicin shine a daidai lokacin da Ruqayya ke cikin firgici da barazana sai kuma muka ga gidan talabijin din da take wa aiki sun saki takardar dake cewar Ruqayya ba ma’aikaciyar su ...