Za Mu Kama Duk Wanda Ya Dauki Makami Ranar Zabe A Kano —’Yan Sanda
Mataimakin babban sufeto-Janar na ’yan sanda DIG Hafiz Muhammad Inuwa da ke kula da harkokin zaben shekarar 2023 a yankin jahohin Arewa maso Yammacin Najeriya, ya gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu, da su kauce wa yin wani abu da zai tada hankulan masu zabe. DIG Hafiz M. Inuwa ya bayyana cewa shugaban ’yan sanda Usman Alkali Baba ya umarce su, da su gargadi ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki da su ja wa magoya bayansu kunne gabanin zaben da ke tafe a ranar Asabar 18 ga watan Maris 2023. Ya bayyana hakan ne a Jihar Kano, a ci gaba da shirye-shirye da rundunar ke yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyinsu. Ya kara da cewa fatansu, shi ne a yi zabe lafiya a kammala lafiya, ba tare da nuna siyasa da gaba ba. “Duk wani dan siyasa in dai yana son ci gaban Kano, to zaman lafiya shi ne ci gaban, so ake a zauna lafiya. “Kuma na zo da jawabi, in gargade su, Wallahi ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen maganin duk wani da ya nemi ya tada fitina, “Saboda haka in...