Malamai Da Tsofaffin Soji Ba Sa Kwazo A Jagoranci —Obasanjo
Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce galibi ba a samun wani ci gaba na a zo a gani a jihohin da suka kasance karkashin jagorancin malamai ko tsofaffin soji. Obasanjo ya ce babu wani ci gaban da aka samu a jihohin kasar nan da ke karkashin jagorancin mutane masu rike da matsayin Farfesa ko Dakta da tsoffin sojoji, har ma da malaman makarantu. Tsohon Shugaban na Najeriya na wannan furuci a jawabinsa yayin wani taro kan zurfafa al’adun dimokuradiyya da aka gudanar ranar Alhamis a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Obasanjo ya ce duk da yake an samu wasu jajirtattun shugabannin da ba su da yawa, akasarinsu ba sa iya mulki mai kyau saboda rashin samun mataimaka na gari, abin da ke hana su jagorancin da ake bukata. A cewarsa, rashin tattaunawa tsakanin shugabannin da masu taimaka musu, kan haifar da gibi wajen musayar ra’ayi, matakin da ke hana samun fahimtar juna da hadin-kai wajen cimma manufar ci gaba da ake bukata. Obasanjo ya ce, bayan kwashe shekaru 60 da sa