Posts

Showing posts with the label Gwamna Bago

Matukin Adaidaita Sahu Dan Kano Da Ya Tsinci Kudi Ya Mayar, Ya Samu Tallafin Miliyan 250 Don Yin Karatu

Image
A wani abin da ya yi kama da gasa, matashin nan mai tuka Adaidaita Sahu mai shekaru 23 a Kano, Auwalu Salisu, wanda ya tsinci kudin wani dan kasuwa dan kasar Chadi har naira Miliyan 15  da ya manta su a kekensa tun a 2023, an ba shi tallafin karatu na naira Miliyan 250 har zuwa matakin karatun digiri na uku  KANO FOCUS ta ruwaito cewa, LEADERSHIP Media Group ta yi bikin karamar  Auwalu a ranar Talata a wajen taron shekara-shekara da kuma bikin karramawa a matsayin wanda ya lashe lambar yabo ta ‘Fitaccen matashin matashin shekarar 2023’, saboda nuna gaskiya da ya yi. Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, wanda aka karrama shi a matsayin Gwarzon dan siyasar LEADERSHIP na shekarar 2023, shi ne ya fara ba Awwalu guraben karatu a Jami’ar Baze da ke Abuja har zuwa matakin digirin digirgir. Bayan haka, gwamnan jihar Neja, kuma wanda ya lashe kyautar Gwarzon Gwamnan na LEADERSHIP, Mohammed Umar Bago, ya mayar da martani cikin raha yana mai cewa jam’iyy

Gidan Yari Zan Jefa Duk Wanda Ya Karkatar Da Kayan Tallafi —Bago

Image
Gwamnan Jihar Neja Umar Bago ya ce duk wanda ya kuskura ya karkatar da kayan tallafin da gwamantin tarayya ta bayar a jihar, sai an daure shi a gidan yari, komai girman matsayinsa. Gwamna Bago ya bayyana wa ’yan jarida cewa daga jami’an gwamnati zuwa sarakunan gargajiya, duk wanda aka kama ya karkatar da kayan da gwamnatin tarayya ta bayar domin rage wa talakawa halin matsin da suka shiga a sakamakon janye tallafin mai, to babu makawa gidan yari ne makomarsa. Masu makarantun kudi sun koka kan hana su karin kudin makaranta a Kano Ta’addanci: Ba don taimakon Majalisar Dinkin Duniya ba da mun banu — Tinubu Gwamnan ya sanar da haka ne bayan ya ba da hutun kwana uku domin ma’aikatanta su sami zuwa karbar kayan tallafin da kudinsu ya kai Naira tiriliyan 3.6. Ya ce hutun na ranar Laraba da Alhamis da Juma’a zai ba wa ma’aikata da masu rike da mukaman siyasa damar zuwa mazabunsu domin sanya ido da kuma tabbatar da gaskiya da adalci a wajen rabon kayan. Gwamnan ya bayyana cewa jiha