Posts

Showing posts with the label Fili

Ƙungiyar ɗaliban makarantar FGC ta Kano sun kai ƙara gurin Tinubu bisa zargin yunƙurin wawashe filin makarantar

Image
Kungiyar tsoffin daliban makarantar FGC ta Kano, mai suna FGCKOSA ta aike da ƙorafi ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa abinda ta kira da wawashe katafaren filin makarantar.  Daily Nigerian Hausa ta gano cewa ma'aikatar ilimi ta ƙasa da haɗin gwiwar wani kamfani, Pluck Global Company Ltd. sun kulla yarjejeniyar yanka wa da yin gine-gine a filin, wanda a ke sa ran gobe Litinin za a ƙaddamar da aikin a harabar makarantar . Takardar korafin ta samu saka hannu na haɗin gwiwa da shugaban ƙungiyar na duniya, Shoyinka Shodunke da kuma wasu shahararrun mambobin ta da su ka haɗa da Sheikh Bashir Umar Aliyu, shugaban majalisar ƙoli ta shari'a ta kasa da Sheikh Rabiu Ishyaku Rabiu, shugaban rukunin kamfanin IRS. Sauran da su ka rattaba hannu a takardar korafin sun haɗa da Engr. Suleiman Adamu, Galadiman Kazure, ⁠Alhaji Nasser Ahmed Dan Darman Lokoja da kuma ⁠Abdul Samaad Rabiu, shugaban rukunin kamfanonin BUA. An kuma aike kwafin ta ga shugaban majalisar dattawa, shugab...