Posts

Showing posts with the label Shirin Lafiya

Kwamishinan Lafiya na Kano Ya Bukaci Hukumomin Su Yi Koyi Hukumar KSCHMA

Image
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya yi kira ga Hukumomin da ke karkashin ma’aikatar su yi koyi da kokarin Hukumar Kula da yajejeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) na bunkasa ko sake duba kundin aikinsu domin samar da ingantaccen kiwon lafiya a jihar. Kwamishinan ya yi kiran ne a yayin taron bita na kwanaki 3 da KSCHMA tare da hadin guiwar shirin Lafiya suka shirya domin samar da tsarin yi wa Hukumar hidima domin inganta aiwatar da shirin bayar da gudunmawar kiwon lafiya. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mohammad Nura Yusuf, jami’in yada labarai na KSCHMA a ranar Juma’a. A nata jawabin babbar sakatariyar hukumar ta KSCHMA, Dakta Rahila Aliyu Mukhtar, ta bayyana cewa, hukumar ta gudanar da ayyukanta na samar da ayyukan kiwon lafiya mai sauki da kuma tallafa wa mazauna jihar Kano domin shawo kan matsalar kudi wajen kafa takardar lissafin magani, da samar da kundin tsarin hidima. yana da mahimmanci. Dokta Rahila ta kar