Al Nassr za ta mutunta hukuncin dakatarwar wasanni 2 kan Ronaldo
Kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr a Saudi Arabia ta tabbatar da shirin mutunta hukuncin hukumar kwallon kafar Ingila kan sabon dan wasan da kungiyar ta saya Cristiano Ronaldo game da haramcin wasanni biyu da ke kansa Wani jigo a Al Nassr ya shaidawa AFP yau juma’a cewa tauraron na Portugal mai shekaru 38 ba zai taka leda a wasanni biyu da kungiyar za ta doka nan gaba ba, domin mutunta hukuncin. Tun a watan Nuwamba ne dai, hukumar FA ta dakatar da Ronaldo a wasanni biyu saboda samunsa da laifin jifan wani magoyin bayan Everton da wayar salula lokacin da ya ke shirin daukar hotonsa bayan rashin nasarar Manchester United hannun Everton a Goodison Park. Har zuwa yanzu dai Al Nassr ba ta yiwa Ronaldo rijista ba, kasancewar kungiyar ta zarta adadin ‘yan wasa 8 sa hukumar kwallon kafar Saudiya ta sahale mata saye daga ketare duk kaka. Zuwa yanzu dai Al Nassr ta sayi ‘yan wasan da yawansu ya kai 9 daga ketare ciki har da Ronaldo da ta sayo kan yuro miliyan 200 bayan dan wasan...