Fiye da mutane 85 sun mutu a turmutsitsin rabon kudi a Yemen
Akalla mutane 85 suka mutu, wasu daruruwa kuma suka jikkata, sakamakon tirmtsitsi da aka yi yayin wani taron raba kudade da aka yi a Sanaa, babban birnin kasar kasar Yemen da ke karkashin ikon ‘yan tawayen Houthi. Ya zuwa yanzu mutane 3 aka tsare bisa zarginsu da hannu wajen haddasa tirmitsitsin da sanyin safiyar ranar Alhamis, bayan da daruruwan mutane suka taru a wata makaranta domin karbar kyautar kudin Riyal din kasar ta Yemen 5,000, kwatankwacin dalar Amurka 8 da ake bai wa mutum guda guda, a daidai lokacin da watan Ramadan mai alfarma ya zo karshe. Hotunan bidiyo sun nuna yadda mutanen da mummunan cinkoson ya rutsa da su, suka rika tsala ihu da neman ceto sakamakon kasa motsawar da suka yi, yayin da wasu tsiraru suka rika yunkurin fitar da mutanen da suka ji rauni. Wasu hotunan bidiyon kuwa, sun nuna gawarwakin wasu daga cikin wadanda tirmitsitsin ya rutsa da su ne yashe a kasa, sai kuma tarin takalma da sauran nau’ikan tufafin da aka yi watsi da su, yayin da kuma wani mai binc