Posts

Showing posts with the label Mata

Fiqhun Aikin Hajji: Matsayin Izinin Miji ga Matarsa

Image
✍️ Mansur Sokoto An tambayi Sheikh Muhammad bn Saleh Al-Uthaimin (rh): Idan namiji ya hana matarsa zuwa aikin Hajji ko yana da zunubi? Sai ya amsa da cewa: "Eh, yana da zunubi kam in har ya hana ta zuwa Hajji alhalin sharuÉ—É—an Hajjin sun cika. Yana da laifi. Ina nufin idan misali ta ce masa, ga É—an uwana zai tafi da ni aikin Hajji kuma ina da guzuri ba ni buÆ™atar ka Æ™ara mani kome, alhalin ba ta sauke farali ba. Ya wajaba ya yi mata izini. In kuma bai yi ba za ta iya yin Hajjinta ko ba da izininsa ba, sai fa in tana jin tsoron ya sake ta. A nan kam tana da uzuri". "Al-Fatawa" na Ibnu Uthaimin (21/115). Fiqhun Wannan Fatawa: 1. Aikin Hajji yana da sharuÉ—É—a. Amma idan na farilla ne izinin miji ba ya cikin sharuÉ—É—an. 2. Ko da Hajjin farilla ne, ana buÆ™atar izininsa domin girman haƙƙensa da yake wajibi a kan ta. Idan ta tafi Hajji haƙƙoÆ™insa da yawa za su faÉ—i. 3. Idan Macce ta samu dalilin yin Hajjin farilla wajibi ne Mijinta ya yi mata izini sai idan akwai...

An Wajabta Wa Mata Musulmi ’Yan Sakandare Yin Shigar Musulunci A Borno

Image
Gwamnatin Borno ta wajabta yin lullubi ga ’yan mata Musulmai da ke makarantunta na sakandare a fadin jihar.  Daraktan Kula da Makarantu na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Borno, Bukar Mustapha-Umara, ya bayyana cewa, Æ™arÆ™ashin sabon tsarin, wajibi ne kowace É—alibar sakandare Musulma ta sanya wando da riga da É—ankwali da lullubi a duk makarantar da take a fadin jihar. “Wannan shigar ta zama wajibi ga dukkan É—alibai mata Musulmi a duk makarantunmu na sakandare da ke Jihar Borno. “Amma ga É—alibai Kirista mata zaÉ“i ne; In sun so sa su iya kasancewa da shigar da suke da ita a yanzu ko kuma su canza wando kawai.” Tinubu ya gana da Ganduje a Abuja Da sanin Ganduje Tinubu ya gana da Kwankwaso —Kofa Daraktan ya kara da cewa cewa wajibi ne shugabannin makarantun su tabbatar da bin Æ™a’idojin sabuwar shigar. Ya kuma bayyana cewa sabuwar dokar sanya tufafin dole ga É—alibai Musulmi za ta fara aiki daga zangon karatu na farkon shekarar karatu ta 2023/2024 da ke tafe. Sannan ya yi kira ga iy...