Posts

Showing posts with the label Senegal

Kotun Senegal ta daure 'yan majalisa saboda dukan mace

Image
  Kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a kan ‘yan majalisar dokokin kasar su biyu na bangaren 'yan adawa, saboda samun su da laifin dukar abokiyar aikinsu daga bangaren masu rinjaye. A ranar 1 ga watan Disambar da ya gabata ne dan majalisar dokoki Massata Samb ya yi dirar mikiya a kan wata ‘yar majalisar mai suna Amy Ndiaye, bisa zargin furta kalaman batanci a kan Moustapha Sy, shugaban wata jam’iyyar siyasa da ke cikin gungun ‘yan adawa sannan kuma shehin malamin addinin musulunci da ake mutuntawa a kasar. Wasu hotuna da ake rika yadawa sun nuna yadda Massata Samb ya lafta wa Amy Sy mari a cikin zauren majaliar ‘yayin da abokinsa dan majalisa Mamadou Niang ya sa kafa ya noshi matar a ciki bainar jama’a. Bayan faruwar wannan lamari, an kwantar da ‘yar majalisa Amy Sy a asibiti bayan da bayanai suka tabbatar da cewa tana dauke da juna biyu a lokacin faruwar lamarin, to sai dai a lokacin da yake yanke hukunci, alkali ya yi watsi da zargin yunkurin kisa kamar dai yadda ma