Almundahanar N96bn: Wike Ya Sake Maka Amaechi A Kotu
Gwamnatin Ribas ta shigar da sabuwar kara kan tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, kan zargin yin sama da fadi da Naira biliyan 96. An maka Amaechi tare da Tonye Cole, dan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar bisa zargin sayar da kadarorin jihar. HOTUNA: Masaukin Ronaldo da burwarsa a Saudiyya DAGA LARABA: Dalilin Da Maza Ke Tsoron Auren Mata ’Yan Boko Zacchaeus Adangor, babban lauyan Gwamnatin Jihar Ribas, ya tabbatar da shigar da karar. Nyesom Wike, gwamnan Ribas, ya kafa wani kwamitin mutum bakwai don bincikar Amaechi kan zargin cirar Naira biliyan 96 daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da yake gwamna. Kwamitin ya kuma binciki batutuwan da suka shafi sayar da kadarorin da tsohon gwamnan ya yi. Kwamitin ya gabatar da rahotonsa a 2015 kan binciken, amma Amaechi ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa. A ranar 27 ga Mayu, 2022, wata babbar kotu ta yi watsi da bukatar Amaechi na hana kwamitin gudanar da bincike a kansa. Sakamakon hak...