Zamu Iya Kwatanta Farin Cikinmu Ne Kadai Da Shiga Aljanna- Inji Mahajjatan Najeriyan Da Suka Je Hajji A Karon Farko
Wata alhajiyar Najeriya, Hauwa’u Sa’ad Joda ta ce shiga aljanna ne kawai zai fi dadi fiye da jin dadin da take ji a halin yanzu yayin da take kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin 2023. A tattaunawar da Jaridar Hajj Reporters ta yi da Joda, wata alhaji daga jihar Adamawa, ita ma ta ce ba za ta iya bayyana yadda take ji ba saboda burinta na rayuwa ya cika. Da take zantawa da manema labarai a ziyarar da ta kai garin Uhud daya daga cikin wuraren da mahajjata suka ziyarta don ganin wasu wuraren tarihi, Hajiya Joda ta bayyana cewa ‘yar uwarta Aisha Ahmad ce ta dauki nauyin gudanar da aikin Hajjin. A cewarta, ta kasa danne kukanta a lokacin da ’yar’uwar ta sanar da ita batun zuwa aikin Hajjin bana, inda ta bayyana cewa “ba za a iya misalta abin farin cikin ba saboda burina na rayuwa ya cika.” Da aka tambaye ta game da ayyukan da Hukumar Alhazai ta Jihar Adamawa da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON suka yi mata daga Najeriya zuwa Saudiyya, Joda ta ce komai ya tafi cikin...