Posts

Showing posts with the label Indonesia

Hukumar NAHCON da Hukumar aikin Hajji taIndonesiya zasu hada gwiwa don samun nasarar aikin Hajji na 2023

Image
Daga Mousa Ubandawaki  Gabanin shirye-shiryen aikin Hajji na 2023, Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) tana nazarin tsarin hadin gwiwa da Hukumar Alhazai ta kasar Indonesiya domin bunkasa da karfafa fasahar yada labarai da kuma samar da kudade don inganta ayyukan aikin Hajjin bana. Shugaban NAHCON, Alh. Zikrullah Kunle Hassan, wanda ya jagoranci tawagar zuwa taron ya bayyana cewa, tallafin fasahar sadarwa da na aikin Hajji na da matukar muhimmanci wajen samun nasarar duk wani shiri na aikin Hajji, don haka akwai bukatar a bibiyi tare da karfafa gwiwa."Domin mu tabbatar da lafiya da walwalar Alhazan Najeriya, ba mu da wata mafita face neman wadatar shirye-shiryen mu na fasahar sadarwa daga mafi kyawun duniya, don tabbatar da ingantaccen tsarin aiki." Taron da aka yi a cikin bikin baje kolin ayyukan Hajji da Umrah na kwanaki 4 da ake gudanarwa a cibiyar Super Dome da ke birnin Jeddah inda sama da mahalarta 400 suka halarta na kara karfafa alakar da ke tsakanin kasa