Posts

Showing posts with the label Majalisar Dattawa

Yanzu-Yanzu : An Zabi Akpabio A Matsayin Shugaban Majalisar Dattawa

Image
An zabi dan takarar shugabancin majalisar dattawa na jam’iyyar APC, Godswill Akpabio, a matsayin shugaban majalisar dattawa. Majalisar dattawa, a ranar Talata, ta zabi Goodwill Akpabio a matsayin shugabanta bayan ya samu kuri’u 63 inda ya doke Sanata Abdulaziz Yari wanda ya samu kuri’u 46. Tsohon Gwamnan Akwa Ibom ya taba rike mukamin Ministan Harkokin Neja Delta daga 2019 zuwa 2022, yana wakiltar shiyyar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma. Cikakken labarin zai zo muku nan gaba