Posts

Showing posts with the label Majalisar Dokoki Ta Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na 2024 Ga Majalisar Dokoki Ta Jahar Kano

Image
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya gabatarwa majalisar dokokin jihar daftarin kasafin kudin shekara ta 2024, wanda ya kai Naira Biliyan 350. Kadaura24  ta rawaito Gwamnan ya gabatar da kasafin ne yau juma’a, Inda yace kasafin kudin na shekara mai zuwa ya Kai Naira Biliyan 350, da Miliyan 250 da dubu dari 320 da Naira dari 798. Yace manyan aiyuka an ware musu Naira Biliyan 215 da Miliyan 822 da dubu 194 da Naira 821, yayin da aiyukan yau da kullum aka ware musu Naira Biliyan 134 da Miliyan 428 da dubu 125 da Naira 977 a kasafin kudin shekara mai zuwa. Kasafin kudin an yi masa take da ” Kasafi na Farfado da cigaba”. Gwamnan Abba Kabir yace Ilimi shi ne ya Sami kaso mafi tsoka a cikin kasafin Inda aka kebe masa Naira Biliyan 95 da Miliyan 389 da dubu 577 da Naira 399. Ga yadda aka ware kudaden sauran bangarorin: 1. Lafiya: Biliyan N51.4 2. Aiyukan raya kasa: Biliyan N40.4 3. Noma: Biliyan N11 4. Shari’a: Biliyan N11 5. Ruwa : Biliyan N13.4 6. Mata da matasa : Biliyan N...

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Jaddada Aniyarta Na Hada Gwiwa Da Majalisar Dokoki Ta Kano

Image
Laminu Rabi’u Danbappa, ya bayyana hakan ne yau a lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin majalisar kan harkokin aikin hajji a ofishinsa wanda ya kai ziyarar ban girma ga hukumar.   A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu,Laminu ya kara da cewa Hukumar Jin Dadin Alhazai, tana iya yiwuwa ne kawai idan aka hada hannu da juna domin kare abin da aka damka wa alhazai. A nasa bangaren, shugaban kwamitin alhazai na majalisar, kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar, Honarabul Sarki Aliyu Daneji, ya ce sun kasance a hukumar alhazai domin nuna fuskokinsu a matsayinsu na mambobin kwamitin daga majalisar dokokin jiha. Sarki Aliyu Daneji, yayi kira ga ma’aikatan gudanarwa da su bada hadin kai domin cimma burin da aka sanya a gaba. A nasa jawabin dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Dala a majalisar dokokin jiha Hon Lawan Hussaini Cediyar yan’gurasa ya shawarci hukumar alhaza...