Posts

Showing posts with the label Kansila

KANSEIC Ta Ce 'Yan Takarar Ciyaman Zasu Biya Kudin Fom 10M, Na Kansiloli Kuma 5M

Image
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC, ta sanar da cewa masu neman shugabancin karamar hukuma da kansiloli zasu biya Naira Miliyan 10 da Miliyan 5 a matsayin kudin takara, inda tace ba za a dawowa da kowa kudin ba. Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana hakan yayin gabatar da ka’idoji da jadawalin gudanar da zaben kananan hukumomi a shelkwatar hukumar a yau Alhamis. Yayi bayanin cewa masu takarar shugabancin karamar hukuma dole ne su biya Naira Miliyan 10 a yayin da masu neman kujerar Kansila za su biya Naira Miliyan 5. Acewarsa, ka’idojin da aka fitar yana dauke da abubuwan da aka hana da wadanda aka amince a yi a zaben dake tafe sannan ya gargadi kan ‘yan takara game da karya ka’idojin. Daga cikin ka’idojin sun hada da cewa dole ne duk mai neman shugabancin karamar hukuma ya kai shekaru 30 zuwa sama. Sannan mai neman takarar Kansila dole ne ya kai shekaru 25 zuwa sama kuma ya kasance yana da shedar katin jam’iyya. “Masu neman shugabanc