Labari Da Dumiduminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Kebe Hukuncin Da Za Ta Yi Kan Zaben Gwamnan Kano
Idan dai za a iya tunawa,Dan takarar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna, ya lashe zaben. Kwamitin mutum uku na kotun karkashin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ya kori Yusuf a ranar 20 ga watan Satumba, 2023, bayan ya zare kuri’u 165,663. Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da cewa Yusuf ne ya lashe zaben ranar 18 ga Maris, 2023, inda ta ce ya samu kuri’u 1,019,602 inda ya doke Gawuna wanda ya samu kuri’u 890,705. Sai dai jam’iyyar APC ta tunkari Kotun, bisa zargin tafka magudin zabe. Kotun da ta amince da APC ta soke zaben Yusuf, inda ta kara da cewa sama da katunan zabe 160,000 “ INEC ba ta sanya hannu ko tambari ba. An rage kuri’un Yusuf zuwa 853,939 yayin da kuri’u 890,705 Ganuwa bai shafa ba. Daga nan sai gwamnan ya shigar da kara a gaban kotun daukaka kara. Jam’iyyun APC da INEC da NNPP su ma sun shigar da kara a gaban kotun. A ranar Litinin, babban lauyan gwamnan, Wole Olanipekun SAN (wanda shi ne babban lauyan Tinubu a PEPC), ya bukaci kotun