Akwai Makiyan Tinubu A Fadar Shugaban Kasa – El-Rufa’i
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa akwai makiyan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a Fadar Shugaban da suke kokarin ganin sun kai shi kasa. Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na Sunrise Daily da safiyar Laraba. El-Rufa’i ya ce mutanen, wadanda bai bayyana sunansu ba, sun fusata ne tun lokacin da aka kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani na APC. Ya kuma ce mutanen na fakewa da bukatar ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi abin da ya dace. Ya ce, “Na tabbatar a cikin Fadar Shugaban Kasa akwai masu son mu fadi zaben nan, saboda bukatarsu ba ta biya ba, an kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani. “Wadannan mutanen na kokarin fakewa da bukatar Buhari ya yi abin da ya dace. Zan bayar da misalai biyu; wannan batun na biyan tallafin mai wanda ya ke sa Najeriya ta kashe makudan kudade abu ne da dukkanmu mun dade da amincewa a cire shi. “Sai da ma na tattauna da Shuga...