Posts

Showing posts with the label ASUU

Gwamnatin Soja ta fi ta farar hula tausayin malaman Jami'a - ASUU

Image
Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce gwamnatocin mulkin soja na baya a Najeriya sun fi ta farar hula mai ci a yanzu tausayin su. Ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja, yayin kaddamar da wasu littattafan manyan makarantu guda 50 da wasu marubuta suka wallafa. Hukumar da ke Kula da Manyan Makarantu ta Najeriya (TETFund), ce dai ta dauki nauyin wallafa littatafan. A cewar Shugaban, “A shekarar 1992, lokacin da muka yi yajin aiki, sai muka bukaci a kalubalance mu, mu kawo mafita kan yadda za a samo kudaden da za a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka amince da su. “Haka aka yi kuwa suka kalubalanci ASUU, inda ko kwana uku ba a yi ba muka kawo batun kafa TETFund, wacce kuma gwamantin mulkin soja ta wancan lokacin ta amince. Ni ina ga gwamnatin soja ta ma fi ta farar hula tausayinmu. “Yadda aka yi aka sami hukumar TETFund ke nan. An rattaba hannu a kan kudurin ya zama doka a 1993. Sai da ASUU ta sake komawa yajin aiki a karo na uku kaf