Posts

Showing posts with the label Tantancewa

Shugaban NAHCON Ya Kaddamar Da Tawagar Ma'aikatan Lafiya Na Hajin 2023

Image
Hukumar alhazai ta kasa NAHCON, ta gudanar da aikin tantance tawagar likitocin da zasu kula da alhazai a aikin hajjin na shekarar 2023.  A sanarwar da Mataimakiyar Daraktar harkokin hulda da jama’a ta hukumar Hajiya Fatima Sanda Usara ta fitar, tace an  gudanar da taron ne a yau, 27 ga Afrilu, 2023 tare da kusan masu neman 212 da aka gayyata don tantancewa. Manyan jami’ai karkashin jagorancin Dakta Usman Galadima na Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, wanda kuma shi ne Shugaban Ma’aikatan Lafiya na Hukumar Kula da Lafiya ta Kasa (NMT), sun tantance takardun kwararrun likitoci, masu harhada magunguna da ma’aikatan jinya da za su kafa tawagar NMT. Da yake gabatar da jawabinsa a lokacin kaddamar da yan tawagar da wayar da kan jama’a, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, Shugaban Hukumar NAHCON ya taya ‘yan tawagar guda 230 murna wanda aka zabo su daga cikin  mutane sama da 10,000 da suka nema  Ya umarce su da su dauki zabarsu a matsayin amana daga Ubangiji Madaukakin Sa...