Posts

Showing posts with the label Najeriya

Hajj 2024: Majalisar Koli Ta Addinin Musulunci Ta Najeriya, Ta Bayyana Damuwa Dangane Da Shirin Hajin Bana

Image
Majalisar Koli ta addinin Musulunci a Najeriya ta bayyana damuwa a game da babbar barazanar da ke tattare da aikin Hajjin bana ga al'ummar Musulmi a Najeriya. A sanarwar da Farfesa Mansur Sokoto ya wallafa a shafinsa na Facebook, yace, binciken da majalisar ta gudanar kan shirye-shiryen aikin Hajjin na bana ya nuna akwai wagegen giɓi a game da shirye-shiryen. Wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta ce wa'adin da hukumomin Saudiyya suka ɗiba game da kammala duk wani shiri da ya kamata kama daga biyan kuɗin kujera zuwa sauran shirye shirye, akwai yiwuwar zai iya cika ba tare da maniyyatan bana sun san halin da suke ciki ba na ainihin kuɗin da ya kamata su cika kan kujerar. Majalisar ta ce har kawo yanzu ba a biya kuɗin rabin kujerun da aka ba wa Najeriya ba. "Babban abin damuwar shi ne mutanen da suka fara biyan wani daga cikin kuɗin kujerar aikin Hajjin na bana, har yanzu suna cikin rashin sanin inda suka dosa," in ji sanarwar. Daga bisani majalisar ta ce ta...

Za Mu Sa Kafar Wando Da Masu Ambato Juyin Mulki — Sojoji

Rayuwa ta yi tsada a Najeriya, lamarin da ya sanya wasu fara kiranye-kiranye da sojoji su yi juyin Rundunar Sojin Najeriya ta gargadi masu kiraye-kirayen juyin mulki, sakamakon matsalar tsaro da kuma tsadar rayuwa da ake fuskanta a fadin kasar nan. Najeriya dai na fuskantar matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa mafi muni a tarihi, abin da ya haifar da zanga-zanga a wasu sassan kasar nan. Wasu daga cikin ’yan kasar sun jima suna kiraye-kirayen sojoji su kifar da gwamnatin Tinubu tare da karbe iko kamar yadda aka yi a Jamhuriyar Nijar. Sai dai Daraktan Tsaro na Sojin Najeriya, Janar Christoper Musa, ya ce masu wannan kiraye-kiraye ba sa nufin kasar da alkahairi. Kazalika, dakarun sojin Najeriya za su sa kafar wando daya da masu wannan kiranye-kiranye. Ya ce abin da sojoji za su yi a yanzu shi ne kawai duba hanyoyin samar da sauki da kuma ciyar da kasar gaba, amma ba maganar juyin mulki ba. Da yake amincewa da halin matsi da ’yan Najeriya ke ciki, Janar Musa, ya ce babu inda juyin mulki...