2023: Dalilin Da Ya Sa Muka Tsayar Da Gawuna Takarar Gwamnan Kano– Ganduje
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar sun tsayar da Mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin dan takarar Gwamnan jam’iyyar a zaben 2023 ne saboda kwarewarsa.
Ya ce biyayya da ilimi da kwarewa da kuma kyakkyawar mu’amalarsa da jama’a su ne suka karfafa zaben nasa.
Yana mai cewa, babu wata jam’iyya a Kano da ke da dan takara kwararre irin Gawuna.
Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron gidauniyar da abokin Gawuna ya shirya a Abuja.
“Dokta Gawuna na sane da shirye-shirye da kuma ayyukanmu, kuma mun yi amannar mutum ne wanda zai taimaka wa cigaban al’uma.
“Wannan shi ne irin mutanen da muke raino, wadanda za su yi tsayin daka wajen ci gaba daga inda aka tsaya da kyawawan ayyukan bunkasa al’uma da aka asassa. Inshaa Allah za mu ci gaba da haka.
A cewar Ganduje, “Daya daga cikin abubuwan da muka yi la’akri da su shi ne ci gaba da ayyuka saboda muhimmancin hakan a sha’anin shugabannci.
“Mun tattara bayanan cigaban da muke bukata, kuma muddin aka rasa ci gaba wajen aiwatarwa abubuwa za su watse, ba za mu kai ko’ina ba.”
“Shi ya sa bayan ya tafi ban bukaci sai wani ya fada mini ayyukan da zan aiwatar ba saboda na san komai, kuma ba ni da dalilin yin watsi da su,” in ji shi.
A nasa bangaren, Gawuna ya ce ci gaba daga inda gwamnatin baya ta tsaya shi ne sirrin samun kyakkywan sakamako.
Ya kara da cewa, “Kwarewata na da muhimmanci, kuma a shirye nake in yi amfani da ilimin da na koya na shekaru wajen yi wa jiharmu hidima.”
(AMINIYA)