Posts

Showing posts with the label 'Yan majalisa

Labari Da Dumiduminsa: 'Yan Majlisar Jahar Rivers 27 Masu Biyayya Ga Wike Sun Bar PDP Zuwa Jam'iyyar APC

Image
Akalla ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas 27 cikin 32 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ministan babban birnin tarayya (FCT). Nyesom Wike ya zurfafa. Wani dan majalisar, Enemi George, ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan majalisar 27 na karkashin jagorancin Martin Amaewhule ne. 'Yan majalisar sun yanke Wannan hukuncin ne a yayin zamansu na safiyar ranar Litinin (DailyNews24)

Kotun Senegal ta daure 'yan majalisa saboda dukan mace

Image
  Kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a kan ‘yan majalisar dokokin kasar su biyu na bangaren 'yan adawa, saboda samun su da laifin dukar abokiyar aikinsu daga bangaren masu rinjaye. A ranar 1 ga watan Disambar da ya gabata ne dan majalisar dokoki Massata Samb ya yi dirar mikiya a kan wata ‘yar majalisar mai suna Amy Ndiaye, bisa zargin furta kalaman batanci a kan Moustapha Sy, shugaban wata jam’iyyar siyasa da ke cikin gungun ‘yan adawa sannan kuma shehin malamin addinin musulunci da ake mutuntawa a kasar. Wasu hotuna da ake rika yadawa sun nuna yadda Massata Samb ya lafta wa Amy Sy mari a cikin zauren majaliar ‘yayin da abokinsa dan majalisa Mamadou Niang ya sa kafa ya noshi matar a ciki bainar jama’a. Bayan faruwar wannan lamari, an kwantar da ‘yar majalisa Amy Sy a asibiti bayan da bayanai suka tabbatar da cewa tana dauke da juna biyu a lokacin faruwar lamarin, to sai dai a lokacin da yake yanke hukunci, alkali ya yi watsi da zargin yunkurin kisa kamar dai yad...