Posts

Showing posts with the label Hudu Ari

Zaben Adamawa: An Ba Da Belin Kwamishina Hudu

Image
  ’Yan sanda sun bayar da belin Kwamishinan Zabe na Jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari, bayan da ya yi kwana uku a tsare a hannunsu. ’Yan sanda sun cafke shi ne kan wata sanarwa mai cike da rudani da ya yi  cewa Sanata Aisha Dahiru Binani ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa, alhali ba a kammala karbar sakamakon karashen zaben ba. Tun a lokacin INEC ta soke sanarwar, sannan ta bukaci ya gabatar da kansa a hedikwatarta da ke Abuja, amma maimakon ya je, sai ya yi layar zana. Daga bisani hukumar ta rubuta Shugaban ’Yan Sandan Najeriya wasikar neman ya binciki kwamishinan zaben, kan yamutsa hazon da ya yi. Amma wata wasika da ya aike wa shugaban ’yan sanda, Hudu ya ce ya yi sanarwar ne a bisa doka, saboda dalilan tsaro. A ranar Talala ’yan sanda suka sanar cewa sun kama Hudu, wanda ya ce ba ya nadamar sanarwar da ya ya yi cewa Binani ta ci zabe. Amma kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya sanar a ranar Juma’a cewa rundunar ta bayar da belin kwamishina...

‘Yan sanda sun fara farautar shugaban INEC na Adamawa

Image
Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya umurci wata tawagar 'yan sanda ta yi aiki tare da hukumar zaben Najeriya INEC wajen bincike da kuma gurfanar da shugaban hukumar zabe na jihar Adamawa da aka dakatar Hudu Yunusa Ari. A wata sanarwar da rundunar ta fitar wacce kakakinta Olumuyiwa Adejobi ya sanya wa hannu, babban sufeton ya ce 'yan sanda za su tabbatar sun yi dukkan mai yiwuwa domin gano dalilin da ya sa Hudu aikata abun da ya yi. Ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen gwamna na jihar Adamawa da aka ƙarasa ne sai kwatsam Hudu wanda shi ne kwamishinan zaɓe na jihar, ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen. IGP Usman ya ce a shirye su ke su tabbatar an yi hukunci da ya dace kan dukkan wadanda aka samu da hannu a lamarin da ya faru a Adamawa domin martaba dokokin dimokradiya. Sanarwar ta tabbatar wa 'yan Najeriya da kuma kasashen duniya cewa 'yan sanda za su binciki ayyana Aishatu Binani ta APC da Hudun ya yi tare saur...