Posts

Showing posts with the label Sabbin kudi

DA DUMI-DUMI: Sake fasalin Naira: Kotun Koli ta Dage Sauraron karar da Kaduna, Kogi da Zamfara suka shigar

Image
Kotun kolin Najeriya ta dage ci gaba da shari’ar kan manufar musanya naira na babban bankin Najeriya CBN zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairu domin sauraron kararrakin da jihohi 10 suka hada.   Kotun kolin da ta saurari karar a ranar Larabar da ta gabata ta cika makil da wasu manyan lauyoyi da sauran gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi, Nasir El-Rufai da Yahaya Bello, bi da bi.   A zaman da ya gabata, Kotun ta dakatar da aiwatar da wa'adin ranar 10 ga watan Fabrairu na CBN daga yin kwangilar tsohuwar takardar kudi ta N200, N500 da N1,000.   Jihohin Zamfara da Kogi da kuma Kaduna ne suka shigar da karar gwamnatin tarayya da kuma babban bankin kasa CBN.   Sauran jihohin da suka hada da Neja, Kano, Ondo, Ekiti, su ma sun nemi a shigar da su gaban CBN da gwamnatin tarayya.     An fara zaman kotun inda mai shari’a John Okoro ya jagoranci kwamitin mutum bakwai.   Ya ce bai kamata kotu ta yi watsi da shari’ar da kuma manufarta ba domin ya shafi ’yan Najeriya da ke addabar jama’a.   Jihar L

Buhari ya gana da Emefiele da EFCC kan karancin Naira

Image
  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri  da Gwamnan Babban Bankin Kasar, CBN, Godwin Emefiele da shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa , EFCC, AbdulRasheed Bawa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari  game da halin da kasar ke cikin na karancin takardar kudin Naira Kazalika gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da takwaransa na Kebbi, Atiku Bagudu, su ma sun halarci zaman na yau Talata. An gudanar da wannan zaman ne a daidai lokacin da  ake fama fa matsanancin karancin takardar kudin Naira wanda ya haddasa zanga-zanga a wasu sassan Najeriya tare da kaddamar da hari kan wasu bankuna da jami’an tsaro. A Juma’ar da ta gabata  ne, shugaba Buhari ya roki ‘yan kasarr da su ba shi wa’adin kwanaki bakwai domin magance matsalar karancin takadar Nairar wadda ta samo asali sakamakon shirin Babban Bankin CBN na sauya fasalin Naira 1000 da 500 da kuma 200. Nan da ranar 10 ga wannan wata ne, wa’a

Kotu Ta Hana Buhari Da CBN Kara Wa’adin Karbar Tsoffin Takardun Kudi

Image
  Babbar Kotun Birnin Tarayya ta hana Shugaba Buhari da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, kara wa’adin amfani da tsoffin takardun Naira da aka sauya fasalinsu. Alkalin kotun, Mai Shari’a Eleoje Enenche ya kuma hana daukacin bankuna da ke Najeriya yin duk wata hulda da ta danganci tsoffin takardun kudin ko neman kara wa’adin amfani da su daga ranar 10 ga watan 10 ga watan Fabrairu da muke ciki. Da yake sauraron Æ™arar da wasu biyar daga cikin jam’iyyun siyasa 18 da ke Najeriya suka shigar, alkalin ya bukaci shugabannin bankuna da jami’ansu su kawo dalilan da za su hana a kama su da kuma gurfanar da su a gaban kotu kan zargin su da yin zagon kasa ga tattalin arziki, bisa yadda suke boye sabbin takardun Naira 1,000 da N500 da kuma N200 da CBN ya sauya wa fasali ya kuma ba su, amma suke kin ba wa mutane. (AMINIYA)